Shugaba Buhari tare da tsohn Shugaban kasa, Olushegun Obasanjo

Tshon Shugaban kasa Cif Olushegun Obasanjo, a ranar talata,a wata wasika da ya aikewa Shugaba Buhari mai shafi goma 13, ya shawarci Shugaba Buhari da kada ya yi marmarin sake tsayawa takara a zaben 2019.

A wata sanarwa da mai dauke da kanun “Mafita: Gamayyar kungiyoin ‘yan Najeriya masu fafutuka, Mista Obasanjjo ya bukaci shi da ya yarda kwallonmangwaro ya huta da kuda, tunda dai an riga anga kamun ludayinsa ba yadda aka zata ba.

“Yana da kyau Shugaba Buhari ya rufawa kansa asiri ya sauka daga mulkin nan salun’alun karatun ‘yan kama. Yana bukatar samun nutsuwa domin yaga abubuwan da yayi, sannan ya yi duba na tsanaki, yaga dama da hauni domin ganin yadda tafiyarsa take, ya zama cikin ayarin tsaffin Shugabannin Najeriya yafi masa rufin asiri, ya zama mai bayar da shawara sabida kwarewa da gogewarsa da kuma sanayyarsa, zasu taimakawa Shugabanni na gaba domin cigaban wannan kasar. Tarihi ba zai taba mancewa da shi ba” A cewar sanarwar ta Mista Obasanjo.

KARANTA CIKAKKIYAR WASIKAR TA MISTA OBASANJO

Tunda yake yanzu muna watan farko na wannan shekarar, babu laifi idan na taya ‘yan Najeriya murnar shiga sabuwar shekarar 2018. Ina mai gabatar da wani muhimmin sako a daidai wannan lokacin da naga yafi dacewa na isar da shi, duba da halin da kasarnan take ciki. Na san wasu daga cikinku zasu bukaci su san, “Me ya kawo batun wannan magana da nake yyi na sako na musamman da nake tafe da shi, wanda ni Obasanjo zan gabatar” Babu laifi idan kunyi wannan tambayar a halin da ake ciki.

Amma akwai wani azancin magana na Yarabawa, inda suke cewa, ‘idan junanka kashe kwarkwata, to zaka jima hannunka bai bushe da jini ba’. A lokacin da nake zaune a kauye, duk inda naga kwarkwata sai na kasheta, ka sanya ta a tsakanin farata guda biyu ka matse almura, hakan zai sanya ko da yaushe ka dinga ganin jini da zararka mace kwarkwata. Domin kaucewa samunka kanka kana mai kashe kwarkwata, dole ne ka dauki matakan da zasu rabaka da kwarkwata.

Rashin yin wani katabus a harkar tafiyar da Gwamnati, kama daga batun Yunwa da tsaro da karyewar tattalin arziki, kama karya, kaci baka ci ba. Idan ba’a tashi tsaye wajen dakile wanzuwarsu ba, to hakan ba zai haifarwa da cigaban kasarnan da mai ido ba, rashin abubuwan da zasu hade kan kasarnan, da nuna bangaranci da rashin mutunta wasu sassan kasarnan, shi ne kashin bayan jefa mu wannan halin da muke ciki a yau. Rashin yin wani abun kuzo mu gani da wannan gwamnatin take yi, mutane a ko ina na kukan yunwa, lallai wannan babbar barazana ce.

Shekaru hudu da suka gabata, lokacin da keta katina na PDP, na fada balo balo cewar, na bar yin siyasar jam’iyya, na koma na sanya Najeriya a gaba, da kuma nahiyar Afurka domin taimakon rayuwar jama’a da cigabansu. Tun wancan lokacin na dukufa wajen ganin na yi nazarin halin da al’umma suke ciki, kuma na yi kokarin ganin bakin zaren warware matsaloli da kuma bayar da shawarwarin da zasu kai ga samun mafitar mawuyacin hali. Batun yaki da yunwa da mugun talauci, abu ne da hatta a majalisar dinkin duniya yan bashi kulawa ta musamman. a dalilin haka, muka yiwa Najeriya kyakkyawan tanadin kubutar da ita daga aukawa batun yunwa da fatara, a wani tsari da muka yi na yakar yunwa da fatara nan da shekarar 2025, munyi wannan tun kafin Majalisar dinkin duniya ta fitar da nata tsarin da shekara biyar. Na mayar da hankali sosai akan abinda ya shafi ilimi da kuma samawa matasa aikin yi domin dogaro da kansu, ina cikin wannan sha’anin face face kuma a kusan ko ina, domin bayar da kwarin guiwa ga na baya, da kada su yanke tsammani. A kan wannan batu da nake kai kuma nayi imani da cewar Allah zai taimake ni.

Na gamsu da yin aikin gamayya, domin a gudu are a tsira tare. A mataki na kasashen duniya, muna yin aiki tare da sauran Shugabanni ne, domin bibiyar al’amura tare da nemo musu mafita, tare da karfafawa juna guiwar yin aiki tukuru domin samar da cgaba mai ma’ana da ya hsafi rayuwar al’umma ta ka tsaye,musamman sa sabon dakin bincike da nazarin da muka samar.

Babbar manufar samar da kungiyar bunkasa nahiyar Afurka, wanda wannan sabon suna ne da mu ‘yan Afurka muka smar domin amfanin yankinmu wanda a turance muke kira APP (Africa Progress Panel), muna yin aiki ne domin samarwa da wannan nahiya tamu abubuwan cigaba masu ma’ana,kuma muna ayin aiki ne tare da dukkan sauran Shugabanni kasashen nahiyar Afurka. Haka kuma, cikin girmamawa na karbi gayyatar majalisar dinkin duniya da ta yi min, daga ofishin babban sakatare janar, inda ya bukaci na zama mamba cikin mutum 18, domin aikin bayar da shawara da kuma sasanta tsakanin al’umma. Bayan haka, akwai ayyuka masu yawan gaske, wadan da nake ciki a kungiyoyi da dama domin wannan nahiya tamu ta Afurka. Domin samun cigaban nahiyar Afurka, dole ne Najeriya ta zama a sahun gaba, wannan kuma yana nuna cewar, dole ne Najeriya ta zama kasa mai amfanarwa ga ‘yan cikinta da kuma na wajenta. Babu wata tantama, yanayin da muke cikin shekaru goma da suka gabata, ba mai dadi bane, mun kasa warware matsalolin kanmu ballantana mu shiga sabgar wasu muyi ruwa muyi tsakai.

Dukka irin wadannan matsaloli da ma wasu da ban fada ba, suna daga cikin dalilan da suka sanya na tsame kaina daga cikin harkokin siyasar jam’iyya, a sabida haka na bar PDP, ko a zaben da ya gabata, ‘yan adawa na marawa baya.  Nayi hakan ne kuwa da kyakkyawar niyya, domin na fahimci hakan ne kadai mafita ga Najeriya. Kamar yadda kowa ya sani ne, shekaru uku da suka gabata, bukatar ‘yan najeriya na su samarwa da kasarnan canji shi ne yayi kanshin turare dan goma. Ni kam, babu wata bukatar kashin kai da nake da ita, dukkan abinda nake yi ina yinsa domin masu tasowa nan gaba, a nan gida Najeriya da kuma nahiyarmu ta afurka. Ko da ku shi wanda yake bisa kan karaga, wanda nake girmamawa, ya gamsu, kuma ya tabbatar ina tare da shi da gaskiya da amana, domin a bainar nasi ya bayyana kurakurensa, wanda hakan ya kara masa martaba. Yana da rawar da zai taka, domin samar da kyakkyawar Najeriya abar alfaharin kowa, dama nahiyar Afurka baki daya wanda duk mutanenta zasu yi alfahari da ita. Asabida hakanake ganin mutuncinsa da kimarsa, amma dai bana fatan sake mara baya ga na kan karagar nan, domin gazawarsa bayyananniya ce.

Irin mawuyacin halin da aka shiga a baya, ya sanya ‘yan Najeriya suka gwammace su mayar da dan uwana Jonathan gida, domin abin yafi karfinsa. Da farko na fahimci cewar, nasan inda Shugaba Buhari yake da rauni, na yi magana kuma na rubuta kan haka, tun kafin ma ‘yan Najeriya su zabe shi, sabida a lokacin nan ba mu da wani zabi illa mu marawa Buhari baya, domin mun ga cewar Mista Jonathan ba shi ne mafitar halin da kasarnan take ciki ba. Amma a lokacin nan, na rubuta wasika zuwa ga Shugaba Jonathan, inda nayi mata take “Kafin lokaci ya kure maka” na rubuta masa da kyakkyawar niyya domin ankarar da shi kafin lokaci ya kure masa. A lokacin bai ji magana ta ba, kuma dai ta bayyana cewar lokaci ya kure masa, wasu ‘yan tsiraru suka yi ta masa romon baka, inda suka zuga shi yayi fatali da shawarwarin da na bashi. Ni fa a yadda nake, babu wani abu da zai yi min barazana, babu wanda zan ji shakkar gaya masa magana ko da kuwa akwai barazana da tunanin za’a halaka ni, domin abinda na gamsu shi ne, zan iya bayar da jini na domin cigaban Najeriya.

Babu wani jagoran wata al’umma da za’ai masa zaton rauni akan tsarin da ya sanya a gaba domin tafiyar da rayuwar mutane. Na san Shugaba Buhari sosai tun ma kafin ya zama Shugaban kasa, na san yana da rauni sosai ta fannin fahimtar rayuwa da batun tattalin arziki, amma abinda nayi zato shi ne, zai yi amfani da kwararrun mutane domin sanya Najeriya akan turba, na san da cewar, ba zaka taba yin kyauta da abinda ba ka da shi ba, haka kuma, tsarin tafiyar da tattalin arziki na yanzu ba irin na zamanin mulkin kama karya bane na soja. Dole ne a saurari shawarwarin kwararru kan batun tattalin arziki domin samawar da al’umma mafita. Daga nan ne kuma za’a fahimci inda za’a sanya gaba, tabbas, na san irin gazawar Buhari akan batun ilimi da mu’amalar Diflomasiyya, akwai ‘yan Najeriya da suke da kwarewa sosai da za’a yi amfani da su domin cire suhe daga wuta. Suna da ilimi da gogewa ta fannoni dabana daban, wanda zasu taimaka wajen cito Najeriya daga aukawa mawuyacin hali. Akwai zarge zarge masu karfi da suke nuna cewar, wasu mutane a fadar Shugaban kasa, sune suke aiwatar da komai a kasarnan. Ina mamakin yadda za’a yaki cin hanci da rashawa a Najeriya, amma an bar wadancan mutane suna cin karensu babu babbaka? Duk wanda yake son tabbatar da gaskiya da adalci tilas ne ya siffanta da abinda yake kira a gareshi, babu yadda za’a wasu mutane a fadar Shugaban kasa,sune zasu dinga aiwatar da komai, kuma ana sansu ana ganinsu, sannan kuma ace akwai gaskiya da adalci a tsarin tafiyar da mulkin wannan kasa.

Da farko nayi zaton Shugaba Buhari zai yi yaki da cin hanci da rashawa cikin gaskiya da nuna babu sani babu sabo, amatsayin nasarorinsa na farko farko wadan da za’a yi bugun gaba da su! Batun rikicin manoma da makiyaya abu ne da za’a iya shawo kansa, amma ana ji ana gani da gangan aka bari abubuwa suka kwabe. Babu yadda za’ayi ace Gwamnatin tarayya tana ji tana gani ta bar Fulani suna yin abinda suka ga dama,sannan a kawar da kai daga garesu, ba tare da anbi hanyoyin kawo karshen wadannan matsalolin ba. Wannan kuma abin takaici ne kwarai, yadda hatta su kansu wasu gwamnoni sun nuna rashin iya mulki ta yadda suka kasa warware irin wadannan matsaloli cikin ruwan sanyi, an binne sama da mutane 73 a kabari daya a jihar Binuwai, amma babu ko ta’aziya daga gwamnati, maimakon haka, sai wasu kidahumai, suka shiga batun wai suna goyon bayan Buhari ya sake tsayawa zabe a karo na biyu. Wannan abin takaici ne kwarai da gaske! Ba zai yuwu a dinga siyasantar da wannan batu na rikicin manoma da makiyaya ba, dole ne Gwamnatin tarayya ta tashi tsaye domin ganin ta kawo karshen dukkan irin wadannan matsaloli da suka addabi kasarnan, domin babu yadda za’a ayi rayuka da dukiyoyin mutane suna salwanta kuma a zauna a zurwa sarautar Allah ido.

Akwai wasu abubuwa da Shugaba Buhari yayi guda uku,wadan da mu kanmu ya shammace mu akan fahimtar da muka yi masa. Rashin yin ko inkula domin kawo karshen matsalolin da suka zo gaban teburinsa, ta yadda ga masu laifi an sansu ana ganinsu amma ba’a iya hukunta su. Wannan kuwa ba karin zubar da kimar Gwamnatin da yake jagoranta bane. Wannan ya nuna yadda ake nuna bambanci da fifiko kan abinda ya shafi kasa baki daya da kuma bukatun tsiraru. Yanzu sabida Allah, taya za’a ce akwai gaskiya a tsarin tafiyar da Gwamnatin nan,idan aka kalli badakalar MAINA: An nuna, kama karya, da rashin bin gaskiya da kudundune, sabida ba’a son a hukunta mai laifi watakila sabida yana da uwa a gindin murhu. Yanzu sabida Allah, matsaloli nawa ne a kasarnan irin wannan, wadan da aka yi shakulatun bangaro akansu? Kowa yayi shiru, da ‘yan jarida da sauran al’umma kowa ya kauda kai akan abubuwan da aka san ba daidai bane?

Abu na biyu, shi ne, rashin kan gadon wannan gwamnai na fahimtar lamura ba tare da sanya SIyasa a ciki ba. Wannan shi ne abinda yake kara raba kan al’ummar kasarnan. Wanda hakan ya shiga hatta cikin sha’anin tsaronmu. Na uku shi ne, kucewa gaskiya. Tayaya za’a ce Gwamnati ta zargi Gwamnan Babban bankin Najeriya da karya darajar Naira da kashi 70 sannan kuma a dinga zargin laifin Gwamnatocin da suka gabata ne, batun da wannan gwamnattin take yi na dora laifin gazawarta kan Gwamnatocin da suka shude, sam ba zai kaita ga tudun mun tsira ba. Kada wani ya rude mu, ana ji ana kallo tsarin tattalin arzikinmu yana neman durkushewa, abubuwa na tafiya ba yadda ya kamata ba. Idan da ace kasarnan komai lafiya lau yake, ai da ‘yan Najeriya basa bukatar sake zuwan Buhari a matsayin Shugaban kasa, ai sabida abubuwa sun baci shi yasa al’umma suka ce sai shi. An zabe shi ne, domin ya gyara al’amuran da suka tabarbare, ba azo ana ta dora laifi a kan Gwamnatocin baya ba. Kundin tsarin Mulkin Najeriya yayi bayanin komai, babban aikin da yake kan Shugaban kasa shi ne, tsayawa kai da fata wajen tabbatar da tafiyar tattalin arzikin Najeriya a bisa turba ta gaskiya, tare da jagorantar hanyoyin da za’a cimma nasara akan abubuwan da aka sanya a gaba. Tsarin da ake kai na fifita wasumakusanta akan halin da kasar take ciki, ba zai taba haifar mana da da mai ido ba.

Rashin lafiyar da Shugaba Buhari yayi, ta sanya da yawan mutane suka tausaya masa, wannan ta sanya aka shiga yi masa adduah babu dare babu rana, wannan kuma dabi’armu ce mu ‘yan najeriya tausawa mara lafiya tare da taimaka masa da adduah. Da yawan ‘yan Najeriya sunyi masa adduah a lokacin da yake jinya a landan, wanda ya shafe fiye da kwanaki 100, duk da cewar ya baiwa mataimakinsa damar cigaba da gudanar da al’amura a madadinsa. Munyiwa Allah godiya da ya dawo mana da Shugabanmu gida lafiya, ko ma dai yane, rashin lafiyar Buhari, shi ta shafa, amma ‘yan Najeriya sun nuna masa kauna da soyayya ta hanyar yi masa adduoi da kuma tausayawa halin da yake ciki a matsayinsa na majinyaci. Amma ba gaskiya bane, yadda wasu makusantansa ke nuna masa suna kaunarsa fiye da kowa, har suna tunanin idan babu shi to Najeriya ta gama yawo. Shugaba Buhari yana bukatar ya yarda kwallon mangwaro ya huta da kuda kawai! Yana bukatar lokaci domin yin nazarin abubuwan da yayi masu kyau da marasa kyau, ya koma ya bi sahun tsaffin SHugabannin Najeriya, shi ne yafi zamar masa alheri, wanda za’a amfana da gogewarsu da shawarwarinsu.  In yayi haka, tarihi ba zai taba mantawa da shi ba, domin kuwa tsarin gudanar da Najeriya batu ne da bashi kamar ya kare, domin yana bukatar mutum mai koshin lafiya sosai, da zai iya sadaukar da dukkan lokacinsa wajen ganin abubuwa sun tafi yadda ya kamata. Ina mai baiwa dan uwana Buhari shawarar cewar, kada wani ko wasu su yi masa romon bakar sake tsayawa zabe a shekara mai zuwa, abinda yafi bukata yanzu shine hutu. Ina yi masa fatan alheri da samun karin koshin lafiya. Ba lallai bane, sai Shugaba Buhari ya karbi wannan kira nawa ba,amma lallai dandanonmagani ba shida dadi, amma dai shi ne abinda tilas a baiwa marar lafiya idan ana kaunarsa. A halin da muke ciki yanzu, Najeriya na bukatar samun cigaba mai ma’ana, kuma ‘yan Najeriya na bukatar gani a kasa. Na sha fada a gurare da dama, cewar jam’iyyun APC da PDP ba sune mafitar wannan kasar ba, domin babu komai a cikinsu sai abin takaici, domin kuwa babu wani bambanci tsakanin jam’iyyun biyu.

Ba zamu taba nade hannu mu zurawa sarautar Allah ido ba. Domin kuwa da jam’iyyun PDP da APC babu wani kare da ba bare ba, batu ne na zabi tsakanin abu guda shida da kuma ace maka wannan rabin dozin ne, kaga ai ba cinya ba kafar baya ne kawai, domin da APC da PDP duk shaidanu ne. Basu kamaci sake komawa karaga ta bin doron bayansu ba, idan kuwa haka ne to meye abin yi? Na iya tunawa Farooq Kperogi, wani kwararren malamin jami’ah a Georgia ta kasar Amurka, ya kira halin da ake ciki da cewar “a cruel Hobson” ba zai yuwu mu zauna kawai muna karatun dan kama ba, tilas mu nemarwa kasarnan mafita.

Na yadda cewar, tsarin da mukekai yanzu shi ne mafi muni tunda kasarnan ta koma kan turbar demokaradiyya a shekarar 1999. Kasar na tafiya a murgude, mutane na cikin dimuwa da bagauniya, babu wani abu da yake nuna cewar gobenmu ingantacciya ce. Bakin hadari ne ya tunkar mu ya turnuke sararin samaniyar kasar, ta fannin Siyasa, tattalin arziki da kuma walwalar jama’a. A lokacin da muke Gwamnati, farashin ganganr manefutr bai wuce $9 ba, kuma muna da kusan bashin biliyan $35. Mutane da dama, na cikin tararrabin halin da kasar ta shiga, abinda ya kubutar da Gwamnati a lokacin, batun hadin kan kasa, wanda aka sanya shi ne farko. Mun kira kowa tare domin a gudu tare a tsiraa tare. Munyi amfani da kwararrun mutane anan gda Najeriya da kuma kasashen waje, ta haka bakin hadarin da ya hado mana,muka ga washewarsa. A wancan lokacin mutane da yawa sun yanke tsammani, amma bamu yi kasa a guiwa ba, mukai ta baiwa mutane kwarin guiwar fita daga mawuyacin hali a kasarnan. Mutane suka ga babu wani Sarki sai Allah, suka yi ammana da mu, muka hada kan kasarnan. Halin da muke ciki a yanzu, batu ne na zabinmu,in munga dama zamu kuma iya canzawa.

Kusan duk inda naje a duniya, ina jin ‘yan Najeriya na ta korafi, wasu ma far fishinsu suke nunawa a fili na halin da ake ciki. AMma kuma duk inda zamu nuna fushinu da damuwarmu, dole muyi komai sannu sannu. Idan mun hada karfi da karfe muna iya samun mafitar wannan halin da muka tsinci kanmu a ciki. Dole mubi hanyoyi nalalama da doka ta yarda da su domin samun mafita, ta hanyar tattaunawa mai ma’ana da fahimtar juna cikin tsanaki zamu iya gano bakin zaren. Muna bukatar sake zage dantse, mu hada karfi da karfe, ta hanyar amfani da mutanan kirki masu gaskiya da amana, domin kubutar da wannan kasar. Wannan lokacin da muke ciki ba batu bane na dora laifin su waye suke da alhakin lalacewar kasarnan, dukkanmu munyi imani abubuwa suna tafiya ba daidai ba, to ya zama tilas a garemu mu nemo hanyoyin fita daga wannan halin. Da farko mu gamsu cewar, wannan Gwamnati ta yanzu tayi iyakar abinda zata iya, dole wannan gwamnatin da jam’iyyar da ke mulki su yadda da mu cewar, sunyi abinda zasu iya,amma halin da suka sanyamu a ciki ba shi ne muke bukata ba. Su sani babu yadda zasu iya bayar da abinda ba su da shi, to su yarda da gazawarsu.

A yanzu Najeriya na bukatar tsayayyen mutum jajirtacce, wanda zai iya sadaukar da komai nasa domin bunkasar kasarnan. Mu nemi wadannan mutanen da suka gaza, da su sake jaraba sa’a, to mu sani babu inda zamu matsa daga inda muke.  Idan ma muka yi sa’a basu wargaza kasarnan ba, to mu godewa Allah.

Wani masanin Falsafa, Einsein, ya gaya mana cewar,  muyi abu iri daya tare da tunanin samun sakamako daban daban, wanna yaudarar kai ne kawai. Yanzu fa, ‘yan Najeriya da kansu, sun soma daukan matakin kashe kansu, sabida tsananin mawuyacin halin da suke ciki. Domin babu wata walwala a tattare da tsarin tattalin arzikin kasarmu. Amma duk da haka, mutane na ywiwa kasar fatan alheri. Abinda kuma muke gani daga ‘yan adawa na kara tabbatar mana cewar, bamu rabu da bukar ba, domin dai duk kanwar ja ce.  Zan iya bugun kirji nace, babu wani abu ku zo mu gani da aka tanadarwa Najeriya.

Muna bukatar canji wanda zai sanya nutsuwa da kuma gamsuwa a zukatan ‘yan Najeriya. Matasanmu suna bukatar basu kulawa domin baje kolin basirar da Allah yayi musu a hanyar irin abubuwa da zasu iya kirkirowa da kuma zurfin ilimi da Allah ya basu. Dole ne a tafi da matasa a wannan halin da ake ciki, matukar muna son cigaba mai dorewa, domin kuwa wadannan matasan su ne Shugabannin gobe. Canji wanda yake da ma’anar, dogaro da kai, da samun daukakar rayuwa, shi ne irin canjin da al’umma zasu yi na’am da shi.  A halin da ake ciki,ana zaman ‘yan marina, ‘ya ‘yan mowa da na bora, wanna ba zai yuwu ba, dole a baiwa kowa dama iri daya, ‘yan Najeriya duk daya ne, babu wani wanda yafi wani fifiko.

Idan aka samu tasgaro a tsarin gudanar da mulki, dole ne suma al’ummar da ake mulka su samu tasgaro, daga nan za ai ta samun karairayi daga bangaren masu mulki domin kare gazawarsu. Abinda ya kamata mu sani kuma mu sakankance akansa shi ne, dole mu yadda fafutikar da magatanmu ska yi domin yau dinmu, ba zata tafi a banza ba.  Allah ma ya san a Najeriya, abubuwa basa wakana yadda ya kamata, a sabida haka ne muka rusuna muka gurfana gabsan, muna neman ya kawo mana dauki ba dan halinmu ba.

Cigaban kasarmu, da zamanantar da harkar tafiyar da Gwamnati ya ta’allaka ne bisa ga yadda muka bayar da kai. Dole ne mu gamsu da wanzuwar ‘yan uwantakarmu, wannan kasar tamu Najeriya na bukatar kowa dakowa domin fitar da ita daga mawuyacin hali, muna bukatar gudunmawar mata da maza da matasa domin cire kitse daga wuta. Muna bukatar hannu da yawa domin yin maganin kazamar miya.

MUNA BUKATAR GAMAYYAR KUNGIYOYIN ‘YAN KISHIN KASA

Irin wannan gamayya a daidai wannan lokacin, bata bukatar sai mun dunwadda kasar zata dogara a garesu. Wannan gamayya bata bukatar  wata ayyananniyar jam’iyya. Muna bukatar zakakuran mutane ne masu zurfin ilimi da gaskiya da sanin ya kamata, domin mu dogara akansu. Irin wannan gamayya da zamu yi, zata kunshi mulkin gaskiya da rikon amana, samarwa da al’umma kyakkyawan jagoranci, da walwala da kuma cigaba. Dole mu ceto kasarnan daga hannu ‘yan bani na iya. A baya mun i adduah, mun kuma bukaci mutane da su bi wannan canji, domin muna zaton na alheri ne. Amma a wannan lokacin, dole ne mu bukaci mutane su yi adduah da fatann Allah ya kawar msu da wannan canji ya kawo na alheri. Kuma Allah zai jikanmu ya kawo mana canji na alheri. Wanna hadaka da zamu yi, bata kunshi goyon bayan wani mutum shi kadai ba, zamu goyi bayan gaskiya ne kawai ko daga wa take, idan har muka kauce daga kan wannan tsarain, muka karkata zuwa ga marawa wani muum baya, to zan fice daga cikin gamayyar, domin ni nayi alkawarin ba zan sake yin jam’iyyar Siyasa ba. Wannan gamayya ko gangami da zamu shirya, zata samu Sakatariyar gudanarwa a babban birnin tarayya Abuja ne.

Wannan gangami da zamu yi, shi ne na digon dambar fitar da Najeriya daga halin da take ciki, tare da dorata akan turba ta gaskiya. Kuma, wannan batu zamu sanya ‘yan Najeriya ne a gaba kawai, musamman matasa da kuma mata. ‘Yan Najeriya masu yiwa wannan kasa fatan alheri, domin baiwa kowa dama iri guda ba tare da nuna bambanci ko wariya ba. Ba zamu bar kasarnan ta balbalce a hannu wasu mutane da bazasu iya amfana mata da komai ba. Da sannu ta hanyar wannan yunkuri namu zamu samar da sabuwar Najeriya, wadda dukkan al’ummar mu zasu yi alfahari da ita.

Wannan gangami zai kunshi abubuwa na cigaba, domin cigaba da dorewar najeriya a matsayin kasa daya al’umma daya. Sanna, ‘yan Najeriya zasu fahimci abinda ake kira tsananin soyayya da mayar da hakali wajen cigaban wannan kasa tamu, dakuma sallamawa dukkan bangarorin kasa baki daya.

Wasu zasu iya tambaya cewar, me kuma Obasanjo yake nema a yanzu? Ku sani, Obasanjo baya bukatar komai, da ya wuce ganin an samu Najeriyar da ‘yan Najeriya zasu yi alfahari da ita.

Ni a matsayin na Obasanjo zan shga cikin wannan gangami, domin kai Najeriya zuwa ga tudun mun tsira. Daga yanzu kasar zata hau turba ta gaskiya, wadda aka aza harsashinta akai. WAnnan gangamin gamayya da zamu yi irinsa ne na farko, domin ceto najeriya daga aukawa wawakeken ramin da ta tunkare shi gadan gadan. Muna fatan Allah ya cigaba da taimakonmu, kuma ya bamu Nasara akan abinda muka sanya a gaba.

 

LEAVE A REPLY