Atiku Abubakar

Tawagar yakin neman zaben Atiku Abubakar a matsayin Shugaban kasa karkashin kungiyar ‘The Atiku Leadhership Development Initiative’ ta tabbatar da nadin Emmanuel Ani a matsayin kodineta a kasar Andalus wato Spain.

Babbaan daraktan waccan cibiyar ne ya sanar da hakanga manema labarai a birnin Awka na jihar AnambraMista Dominic Nwuzor, inda ya bayyana cewar kungiyar yakin neman zaben na Atiku tana da mutane a dukkan sassan duniya baki daya.

Dominic ya bayyana cewar ya zuwa yanzu babu mutumin da ‘yan Najeriya ya dace su sanya a gaba kamar Atiku Abubakar domin shi ne kadai  mutumin da ya auri Bahaushiya da Inyamura da Beyerabiya a matsayin matansa na aure.

Najeriya na bukatar mutum mai zurfin tunani da sanin ya kamata da fahimtar lamuran kasarnan yadda suke kamar Atiku Abubakar.

 

LEAVE A REPLY