Shugaban jam'iyyar PDP na kasa Uche Secondus wajen gamayyar jam'iyyun adawa a Shehhu YarAdua

Jam’iyyar PDP da SDP da kuma sabuwar APC da wasu karin jam’iyyu 36 sun amince su kulla wata gamayyar da zata yi sanadin raba jam’iyyar APC da mulkin Najeriya a kakar zabe ta shekarar 2019.

Shugabannin jam’iyyun na kasa ne suka hadu a cibiyar tunawa da marigayi Shehu Musa YarAdua inda suka rattaba hannu domin yin aiki tare da juna karkashin gamayyar CUPP wadda zasu tsayar da dan takarar Shugaban kasa guda daya da zai kada Shugaba Buhari.

Jam’iyyun da suka halarci wannan taro domin wannan gamayya sun hada da R-APC da AD da ADC da ADP da AGAP da APP da ACD da BNPP da DA da DPP da kuma jam’iyyar GDPN.

Sauran su ne GPN da KOWA da LP da MAJA da MMN da NCP da NGP da kuma jam’iyyun NUP da NIM.

Ragowar sun hada da PPP da PANDEL da PDC da PPC, haka kuma akwai jam’iyyun RPN da UPN da AGA da NIP da NDC da PPA da kuma jam’iyyar matasa ta YDP.

A lokacin da yake jawabi, Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Uche Secondus ya bayyana cewar tuni ‘yan Najeriya suka jima suna dakon zuwan wannan rana da jam’iyyun zasu yi gamayya domin kayarda jam’iyyar APC mai mulki.

Da yake nasa jawabin Shugaban sabuwar jam’iyyar R-APC Alhaji Buba Galadima ya bayyana cewar tuni kasashen duniya suke ta mamaki ko anya kuwa akwai mazaje da zasu iya tunkarar jam’iyya mai mulki a Najeriya kuwa!

Shima a nasa bangaren Shugaban jam’iyyar SDP na kasa Olu Falae ya bayyana cewar a halin da kasarnan take ciki babu yadda jam’iyyu zasu zuba ido suna ganin Gwamnati da jam’iyyar APC suna yin abinda suka ga dama ba tare da tsawatar musu ba.

LEAVE A REPLY