Ibrahim Badamasi babangida

Cikin kasa da makwanni uku da tsohon Shugaban mulkin soja na Najeriya, Ibrahim Badamasi Babangida da ya rubutawa Shugaba Buhari wata wasika da ta janyo cece-kuce a fadin Najeriya.

Gidan IBB dake saman dutse a Minna, ya karbi bakuncin tawagar Shugabannin jam’iyyar PDP na kasa. IBB dai na daya daga cikin mutanen da suka haifar da jam’iyyar PDP a Najeriya, kuma Shugabannin jam’iyyar na kasa sun kai masa ziyarar a karshen makon nan.

A ranar Asabar din da ta gabata Shugaban jam’iyyar na kasa Uche Secondus ya jagorancin tawagar Shugabannin jam’iyyar zuwa gidan tsohon Shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babanggida, kuma daya daga cikin iyayan jam’iyyar a Najeriya.

Janar Babangida wanda ya Shugabancin Najeriya daga shekarar 1985 zuwa 1993 karkashin kakin soja. Ya yiwa tawagar Shugabannin jam’iyyar ta PDP maraba a gidansa. Bayan tawagar Shugabannin PDP, IBB din ya kuma karbar Shugaban jam’iyyar APC na kasa John Oyegun a gidan nasa a ranar Asabar din.

Mista Oyegun ya shaidawa IBB cewar ya zo Minna ne domin ya karbbi wasu wadan da suka sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jami’iyyar APC,wanda suka hada da tsohon mataimakin Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Aminu Yusuf da kuma tsohon kakakin majalisar dokokin jihar ta Neja Adamu Usman.

 

LEAVE A REPLY