Shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya amince ya kafa wani kwarya kwaaryar kwamiti da zai shiga tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa domin sasanta wagegen sabanin dake tsakani domin samar da zaman lafiya da fahimtar juna.

Jam’iyyar ta cimma wannan matsaya ne a cewar Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Ahmed Lawan, bayan da aka kammala wata ganawa ta musamman tsakanin Shugabancin amintattu na jma’iyyar da kuma masu ruwa da tsakani na jam’iyyar dake majalisar dattawa a ranar Laraba.

Sanata Ahmed lawan ya shaidawa taron ‘yan jaridu cewar, mambobin kwamitin da za’a kafa zasu fito daga cikin Gwamnoni da ‘yan majalisun tarayya da kuma wasu daga cikin bangaren zartarwa, a babbar sakatariyar jam’iyyar za’a kaddamar da wannan kwamiti.

Yace aikin da yake gaban kwamitin shi ne, domin yaga ya rage yawan rashin fahimtar juna da ake samu tsakanin ‘ya ‘yan jam’iyyar a ko ina a fadin najeriya.

Ya cigaba da cewar, rashin fahimtar juna da kuma sabani da ake samu tsakanin ‘yan jam’iyyar yayi yawan da zba za’a nade hannu a tsaya ana kallonsa ba, sasakai ba tare da yin wani abu na kawo karshensa ba.

Zaman tattaunawar dai an yi shi ne tsakanin Shugabancin jam’iyyar na kasa karkashin Shugaban jam’iyyar na kasa John Oyegun tare da tsagin ‘yan majalisar dattawa karkashin jagorancin Shugaban majalisar Bukola Saraki.

LEAVE A REPLY