Shugaba Muhammadu Buhari tare da jagororin mutanan yankin kudu maso gabas

Shugabannin jam’iyyar APC, daga yankin kudu maso gabas wanda ya kunshi Imyamurai zalla, a ranar litinin sun ayyana goyon bayansu ga Shugaba Muhammadu Buhari ya zarce a karao na biyu a 2019.

Jagororin na yankin Inyamurai,, sun bayyana goyon bayansu ga sake tsayawar Shugaba Muhammadu Buhari ne a lokacin da suka yi gangami domin kai masa ziyara ta musamman a ofishinsa dake fadar Gwamnati a Abuja.

Haka kuma, Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC na kasa mai wakiltar shiyyar kudu maso gabas, Emma Eneukwu wanda shi ne ya karanta takardar nuna goyonbayan Inyamurai a madadin tawagar, sun bukaci Shugaba Buhari da ya ramawa kura a niyarta na marawa inyamuri baya ya zama Shugaban kasa a shekarar 2023.

“Wannan wani abu ne da muka amince da shi cewar, shekaru hudu sunyiwa Shugaba Muhammadu Buhari kadan wajen cimma irin abubuwan da yake tafe da su domin aiwatarwa al’ummar Najeriya domin bunkasata”

“Mun amince mu marawa Shugaba Buhari baya, sabida gaskiyarsa da muka gani da kuma tafiya da kowa tare, muna kuma fatan da wannan goyon baya da muka bashi, shima zai goyi bayan shiyyar kudu maso gabas ta fitar da Shugaban kasa bayansa a zaben 2023”

Sannan kuma, sun yabawa kokarin Shugaba Muhammadu Buhari na kawo musu ayyukan raya kasa a yankunansu na kudu maso gabas, musamman babbar hanyar nan ta gadar naija ta biyu da titin Enugu zuwa Fatakwal da kuma titin Enugu zuwa Owerri da sauransu.

Da yake maida martani, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, yasha alwashin yin duk abinda zai iya wajen ciyar da najeriya gaba, tare da sanya tsoron Allah da kishin kasa a gaba.

Ya kuma jinjinawa kokarin na shugabannin Inyamurai musamman na yadda suka fahimci Gwamnatinsa, da sadaukarwarsu da kokarin samar da zaman lafiya a wannan kasa.

Sannan kuma, Shugaban ya kara yabawa Shugabannin bisa yadda suke baiwa Gwamnatinsa hadin kai da kuma goyon baya a ko da yaushe, domin cimma kudurinsa na mayar da Najeriya kasar da kowa zai yi alfahari da ita.

“Ina cike da murna, akan wannan ziyara ta nuna goyon baya da kuka kawo min. Muna sane da kokarin da kuke yi na bayyanawa mutane alheran wannan Gwamnai ba tare da wani shayi ba”

“Ina son na sanar muku cewar, ban mance da wani sashin kasarnan ba,musamman irin yadda kuka nuna min kauna, da goyon bayanku ne na cimma wasu kudurorina masu yawa, naji maykar dadin wannan ziyara taku kwarai da gaske, ko yaushe fatanmu mu bar abubuwan da ‘ya ‘yanmu da jikokinmu zasu gada su san cewar mun bar musu kyakkyawan abin gado”

“Ina mai tabbatar muku da cewar duk wani abu da zan yi, to zan yi shi ne da zuciya daya, ba tare da nuna wariya ko fifiko ba”

DAILY NIGERIAN HAUSA a habarto cewar, daga cikin mutanan da suka halarci wannan taro akwai awagar Gwamnan jihar Imo wanda mataimakinsa Eze Madumere ya jagoranta, sai kuma wakilan zartarwa na jam’iyyar APC shiyyar kudu maso gabas da Ministocin da suka fito daga yankin.

Sauran su ne tsohon Shugaban majalisar dattawa Ken Nnamani da tsohon Gwamnan Ebonyi Martin Elechi da Sanata Andy Uba da Sanata Ben Uwajimogu da tsohon Gwamnan tsohuwar jihar Anambara Jim Nwabado da Sanata Nkechi Nworgu da Sanata Ifeanyi Ararume da tsohon ministan kwadago Emeka Wogu.

Sai kuma Sanata Uche Ekwunife, Hon. Tony Nwoye, Okey Ezea, George Moghalu, Mai binciken kudi na kasa na APC, Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC shiyyar kudu maso gabas, Emmanuel Eneukwu, Cosmos Maduba, Sanata Chris Nwankwo, Chris Adighije, Anthony Agbo, da kuma Emma Anosiki, da tsohon mataimakin Gwamnan jihar Abiya Cosmas Akomas, Nnanna Uzor Kalu, Dr. Uche Ogar.

Sauran wadan da suka halarci taron sune Nnanna Raphael Igbokwe, Chike Okafor, Austin Chukwukere, Sam Nkire, Mac Nwabara, Mataimakiyar shugabar mata ta jam’iyyar APC Tina Ekwueme-Adike, Princess Gloria Akobundu, Shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Imo , Eze Nwosu Da kuma kwamishinan yada labarai na jihar Imo, Prof. Nnamdi Obiaraeri da sauransu.

LEAVE A REPLY