A daidai lokacin da zaben 2019 yake sake karatowa, hukumar zabe ta kasa INEC a ranar Alhamis ta yi kira na musamman ga hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati EFCC da ta sanya idanu kan kudaden da ‘yan Siyasa zasu kashe a lokacin yakin neman zabe.

Shugaban hukumar zaben, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana hakan ne a lokacin da mukaddashin Shugaban hukumar ta EFCC Ibrahim Magu ya kaimasa ziyara a ofishinsa a Abuja ranar Alhamis.

Mista Yakubu ya bayyana cewa “Dokokin da suka kafa hukumar zabe ta kasa, sun yi adadi akan irin kudaden da ‘yan siyasa zasu kashe a lokutan yakin neman zabe, sannan ya kasance za’a iya bibiyar hanyar da suka tara kudin yakin neman zaben”.

“Muna bukatar hukumar EFCC da ta yi kokarin sanya idanu tare da bibiyar dukkan ‘yan SIyasa kan kudaden da zasu kashe. Ba zamu taba zuba idanu ‘yan Siyasa su sayar da Dimokaradiyyar Najeriya ba, ina fatan, idan muka yi aiki da hukumar EFCCzamu cimma hakan”

Shugaban na hukumar zabe, yace suna bukatar hadin kan hukumar EFCC domin dakile yadda ‘yan Siyasa suke sayen masu jefa kur’a a lokacin zabe.

Ya cigaba da cewa “A yayin da shekarar zabe ta 2019 take karatowa, muna matukar bukatar tallafi domin samun aiwatar da wannan zaben cikin aminci”

“Hukumar zabe ta INEC tana cikin kaduwa irin yadda taga ‘yan Siyasa suke sayen masu jefa kuri’a wa wajen jefa kuri’a. ‘Yan takarkaru da shugabannin jam’iyyu suna zuwa wajen zabe da makudan kudade”

A nasa jawabin, SHugaban hukumaryaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC Ibrahim Magu, yace galibin abinda ya sanya ‘yan Siyasa da suke yin hakan shi ne mugun cin hanci da rashawa da yayi katutu.

Yace “Dukkaninmu zamu iya hada hannu domin taimakawa wajen yaki da cin hanci da rashawaa. Cin hanci da rashawa muguwar cuta ce, ta yiwa Najeriya muguwar illa, mun sane da cewar hukumar zabe ta kasa INEC tana yaki da cin hanci da rashawa a kaikaice”

“Mun san cewar hukumar zabe ba zata yaki cin hanci da rashawa kamar yadda mu muke yi a EFCC ba, A sabida haka ne, nake kira a garemu gaba daya da mu yaki cin hanci da rashawa ta duk hanyar da zamu iya tallafawa”

LEAVE A REPLY