Wani jigo a jam’iyyar APC mai mulki a jihar Abiya, Okey Adiaso, ya bayyana cewar babu wani dan takarar da za’a kamanta shi da Shugaba Buhari a zaben 2019 dake tafe.

Mista Adiaso yana mayar da martani ne akan wani kalami da Shugabannin Arewa karkashin jagorancin Ango Abdullahi suka yi akan Gwamnatin Shugaba Buhari mai ci, yace takarar Shugaba Buhari bata ta’alla da sahalewar Shugabannin Arewa kadai ba.

Da yake magana da ‘yan jarida a kauyensu Obichukwu a yankin karamar hukumar Isiala Ngwa ta kudu a jihar Abiya, Mista Adiaso ya bayyana cewar Shugabannin Arewa da kungiyoyinsu suna bayyana ra’ayoyinsu ne kawai. Ya kara dacear, ra’ayoyinsu ba shi ne ra’ayoyin al’ummar Najeriya ba.

Ya bayyana wadannan ra’ayoyi na SHugabannin Arewa da cewar ra’ayi ne kawai na fusatattun ‘yan adawa, wanda suka san cewar Shugaban kasa ya jika musu aiki.

Kungiyar Shugabannin Arewa wanda suka yi babban taronsu a karshen mako a jihar Kaduna, sun bayyana cewar sambasu gamsu da yanayin yadda Gwamnatin Shugaba Buhari take tafiya ba, sabida bai tsinanawa yankin Arewa komai ba. Haka kuma, Shugabannin sun yi Allah wadai da kashe kashen da ake yi a yankin Arewa. Shugabannin kuma, sun bayyana cewar zasu cigaba da kare martabar Arewa.

LEAVE A REPLY