Atiku ABubakar tare da Dankwambo

Tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya kai ziyara ga Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hasan Dankwambo. Tsohon Mataimakin shugaban ksar yana jihar ne a cigaba da zagayen da yake yi na tuntuba kan batun takararsa ta Shugaban kasa a kakar zaben 2109 dake tafe.

Atiku Abubakar tare da Ibrahim Dankwambo kusan su ne mutane biyu da ake ganin sun nuna aniyar yin takarar Shugaban kasa da suka fito daga yankin Arewa maso gabas da ya ssha fama da rikicin ‘yan kungiyar Boko Harama.

Dukansu biyu dai na neman takarar Shugabancin Najeriya a karkashin tutar jam’iyyar PDP mai hamayya. Shin waye kuke ganin zai hakura ya janyewa wani a cikinsu?

LEAVE A REPLY