Gwamnan jihar Kaduna Mallam nasiru el-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai a ranar Juma’a ya nada sabbin Kwamishinoni guda biyu a majalisar zararwa jihar, bayan ya dan yi wasu sauye sauye a majalisar zartarwar jihar.

Kamar yadda wata sanarwa da mai taimakawa da Gwamnan kan ‘yan Jaridu Samuel Aruwan ya tabbatarwa da manema laarai. Gwamnan yayi wadannan canje canje ne bayan mutuwa kwamishinan ilimin jihar Mista Andrew Nok.

Sabbin kwamishinonin su ne:

  • Madam Ruth Geoffrey Alkali, Ma’aikatar Ciniki, Masana’antu da Yawon bude Ido
  • 2. Dr. Ibrahim Hamza, Tsohon Daraktan hukumar KADFAMA, wanda yanzu aka bashi Ma’aikatar Albarkatun Ruwa.

Sauran Kwamishinonin da suka samu sabbin ma’aiktu su ne:

3. Dr. Manzo Maigari wanda aka dauke daga Ma’aikatar Ciniki, Masana’antu da Yawon bude Ido zuwa Ma’aikatar Ayyukan Gona
4. Professor Kabir Mato wanda aka dauke daga Ma’aikatar Ayyukan Gona zuwa Ma’aikatar kananan hukumomi
5. Ja’afaru Sani daga Ma’aikatar kananan hukumomi zuwa Ma’aikatar Ilimi da Kiimiyya da Fasaha
6.Balaraba Aliyu-Inuwa daga Ma’aikatar Raya Karkara da cigaban al’umma zuwa Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje da kuma Sufuri
7. Hassan Usman Mahmud daga Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje da kuma Sufuri zuwa Ma’aikatar Raya Karkara da cigaban al’umma

Sauran Kwamishinonin da suka cigaba da rike ma’aikatunsu sune:
8. Umma Hikima, Ma’aikatar Shari’ah
9. Suleiman Abdu Kwari, Ma’aikatar Kudi.
10. Dr. Paul Dogo, Ma’aikar Lafiya
11. Muhammed Sani Abdullahi, Ma’aikatar Kasafi da Tarse-tsare
12. Amina Dyeris Sijuwade, Ma’aikatar Muhalli.
13. Daniel Amuze DanAuta, Ma’aikatar Matasa da Wasanni.
14. Hafsat Mohammed Baba, Ma’aikatar Mata da Cigaban jama’a.

LEAVE A REPLY