Rahotanni daga hukumomin tsaro na kasa da suka hada da DSS, sun tabbatar da cewar kungiyar IS masu gwagwarmayar kafa kasar Musulunci reshen Afurka ta yamma, sune suke da alhakin kashe kashen da aka yi a jihohin Binuwai da yankin Arewa ta tsakiya da kuma kudu maso kudu a Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ta ruwaito cewar, wani rahoto da fadar Shugaban kasa ta karba daga hukumomin tsaro ya tabbatar da hakan ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Rahotanni sun tabbatar da cewar, kungiyar ta IS reshen Afurka ta yamma, suna da mutanen daga wajen Najeriya da suke amfani da su domin kai miyagun hare hare domin kashe mata da kananan yara, wanda hakan ya jefa kasar cikin rudani dangane da barkewar fadan kabilanci.

A cewar fadar Shugaban kasa, majiya mai tushe ta tabbatar da cewar a sakamakon kame kamen da aka yi dangane da kashe kashen da aka yi wanda ake zargin Fulani da yinsu a jihar Binuwai.

Majiyar ta kara da cewar, daga cikin wadan da aka kame din, da yawansu basa iya magana da yrukan da ake yinsu a cikin Najeriya, galibinsu suna magana ne da harshen Faransanci.

“Wannan shi ne karon farko da jami’an tsaro a Najeriya suka tabbatar da cewar, akwai ‘yan kungiyar Is reshen Afurka ta yamma suna gudanar da al’aamuransu a Najeriya, kuma suna shirin kawo rudanin da ka iya yamutsa kasar”

Majiyar ta kuma cewar, an kama da yawa da ga cikin ‘yan kungiyar ta IS reshen Afurka ta yamma, ba wai kawai an kama su a jihohin Binuwai bane, har da Edo da Koi da sauran kauyukan dake jihohin.

“Zamu iya fahimtar hakan ta kallon yadda ake zubar da jini bayin Allah babu gaira babu dalilin domin kawai yunkurin yamusta kasarnan da kokarin tunzura mutane su dauki makamai suna yakar junansu”

“Kungiyar tasu, tana da karfi sosai, amma tuni hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta tabbatar da kam da yawa daga cikinsu a cikin watanni biyu, wanda hakan ya taimakawa hukumar wajen samun bayanai”

“Samun wadannan bayanai ya taimakawa Najeriya kaucewa fadawa cikin mummunan rikicin kabilanci wanda kungiyar ta IS reshen AFurka ta yamma ta so jefa kasarnan a ciki”

NAN ta tabbatar da cewar, bayanan da aka gabatarwa da fadar Shugaban kasa, shi ne cewar, jami’an tsaro sun fara soron yaduwar ‘yan kungiyar tsakanin ‘yan Najeriya a sassan kasar daban daban.

“Muna kara fahimtar irin yadda ‘yan kungiyar suke da kaarfi wajen sadarwa a tsakaninsu”

“Wannan shi ne babban dalilin da ya sanya hukumaar tsaron kasa ta farin kaya ta ki yadda ta gabatar da mutanan da aka kama domin nuna su gaban ‘yan jarida. Domin wannan ya nuna cewar Najeriya na fuskantar barana ta tsaro mai girman gaske”

A lokacin da aka tuntubi mai magana da yawun fadar Shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya tabbatar da cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi wannan rahoton kan irin yadda aka gudanar da kashe kashe a jihar Binuwai da sauran jihohi.

A cewarsa, Hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS ta cimma nasara mai yawa a baya bayan na, sai dai ya bayyana cewar bai samu cikakken rahoton ba balle yace wani abu.

NAN

LEAVE A REPLY