Shugaban ƙasar Kenya Uhuru Kenyatta dauke da yaron da yayi kira a gare shi da ya Musulunta

Wani yaro dan kimanin shekaru 6 da haihuwa ya bukaci shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta da ya karbi addinin Musulunci. Yaron ya bayyana wannan kiran ne ranar litinin a fadar Gwamnatin Kenya dake Mombasa a lokacin da ya kaiwa Shugaban kasar ziyara.

Yaron wanda aka sakaya sunansa, dan makaranta ne, kuma ya isa fadar Gwamnatin ne tare da mahaifiyarsa wanda su Musulmi ne. A yayin ziyarar, anga Shugaba Kenyatta dauke da yaron a hannunsa, suna dariya shi da yaron.

“Ina son kasance da kai, kada ka damu Shugaba Kenyatta, Ina son kasancewa da kai” Yaron ya fada ya kuma maimaitawa Shugaba Uhuru Kenyatta. Kafin daga bisani, Shugaba Kenyatta ya shigar da yaron cikin ofishin Shugaban kasa, sannan kuma ya bashi kujerar Shugaban kasa yaron ya zauna. Bayan da yaron ya zauna ne, sai shugaba Kenyatta yace masa “kaima zaka iya zama Shugaban Kenya nan gaba”.

Yaron ya fadawa Shugaba Kenyatta “Kai shugabanmu ne, ko ba kai bane Uhuru Muigai Kenyatta, zamu ji dadi idan ka kasance Musulmi, kuma zaka iya Musulunta, zamu ji dadi sosai” A cewar yaron.

Shugaba Uhuru Kenyatta tare da mataimakinsa WilliamSamoe Ruto bushe da dariya a lokacin da yaron ya bukaci Shugaba Kenyatta da ya Musulunta.

An dai ta yayata wannan ganawa ta Shugaba Kenyatta da wannan yaron a shafukan sada zumunta a kasar ta Kenya, inda mutane da dama suka dinga raha suna tofa albarkacin bakinsu.

 

LEAVE A REPLY