Yarima Muhammad Bin Salman na kasar Saudiyya

Yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya, Muhammad Bin Salman na yin wata ziyarar aiki ta kwanaki uku a kasar Burtaniya.

Ziyarar da Yariman Saudiyyan yake yi a kasar ta Burtaniya zata mayar da hankali ne akan batun tattalin arzikin da ya shafi kasashen biyu, Burtaniya da Saudiyya, sannan ana sa rantattaunawa kan batun yakin da ake yi a Yemen tsakanin Firaministar Burtaniya da kuma Yariman Bin Salman.

An shirya Yarima Bin Salman zai yi wata liyafar cin abincin dare ta kasaita tare da Sarauniya Ezzabul ta kasar Burtaniyar a daren yau.

Sai dai wannan ziyara ta Yarima Bin Salman ta gamu da fushin masu zanga zanga, inda suka yi dandazo a harabar ‘Lamba 10 Downing Street’ domin nuna fushinsu akan yakin da kasar ta Saudiyya take jagoranta a kasar Yemen.

LEAVE A REPLY