Rahotanni daga yankin birnin Qudus na kasar Falasdinu, ya ce an samu ɓarkewar tarzoma yau Juma’a bayan an idar da Sallah. An samu barkewar tarzomar ne tsakanin Falasdinawa Musulmi da kuma Yahudawa ‘yan Israela.

Daman dai ana ta rade radin samun tarzoma tun bayan da Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ayyana birnin na Qudus a matsayin, babban birnin kasar Israela. Tuni dai daman Yahudawa suka mamaye gabar yamma da kogin Jordan da wasu sassa na zirin Ghazza.

Rahotanni daga kafafen yada labarai na kasashen Larabawa na cewar a kalla mutane sama da 200 suka jikkata a sakamakon jefe jefe da harbin barkonon tsohuwa da ake yi tsakanin Falasdinawa da kuma jami’an tsaron Israela.

Zuwa anjima zamu kawo muku cikakken rahoton abinda yake faruwa

LEAVE A REPLY