Shugaban kasar Afurka ta kudu, Cyril Ramaphosa

Daga Hassan Y.A. Malik

Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya bayyana a ranar Larabar da ta gabata cewa ya yanke hukuncin raba albashinsa biyu, inda za a na sanya rabin a wani asusun tallafawa mabukata.

Asusun wanda za a sanyawa suna Nelson Mandela Thuma Mina Fund zai kasance ne a karkashin asusun Nelson Mandela, kamar yadda shugaban ya fadawa ‘yan majalisar kasar a yau.

Ya ce banda na shi albashin, za a janyo hankalin ‘yan kasar da za su iya bada wani kaso na albashin su domin a yi amfani da su waje yin kananan ayyukan da ke gina kasa.

Ramaphosa dai ya na daukan albashin rand miliyan 3.6 wanda ya yi daidai da dala 293,000 a kowacce shekara.

LEAVE A REPLY