A karon farko a tarihi, kasar Saudiyya ta bayar da dama ga mata su shiga aikin Soja. A ranar Alhamis din da ta gabata ne, a hukumance kasar Saudiyya ta baiwa mata damar shiga aikin Soja a biranen Riyadh da Makkah da Al-Qassim da kuma madina.

Wannan dai wata dama ce da aka baiwa mata da zasu bayar da tasu gudunmawar a harkar da ta shafi tsaro a kasar.

Akwai sharuddan da hukumomi suka gindaya akan matan da suke son kasancewa sojoji a kasar, daga ciki sun hada da: “Dole mace ta zama ‘yar asalin Saudiyya, sannan ta kasance mai shekaru 25 zuwa 35 sannan ta mallakai shaidarkammala diploma a kalla.

Haka kuma, dole ne macen da ke son Shiga aikin soja ta gabatar da wani muharriminta wanda zai tsaya a madadinta. Sannana shi ma dole ne ya kasance dan Saudiyya kuma da yake zaune a kasar.

Wannan hukunci da kasar ta yanke na baiwa mata damar shiga aikin soja, na daga cikin irin sauye sauyen da Gwamnatin kasar take samarwa domin tafiya da zamani.

Hakakuma, wani dan rajin kare hakkin bil adama a kasar, ya bayyana cewar sanya Muharrami cikinsharuddan kasancewar mace soja abu ne da ya dace.

Haka kuma, dokokin sun tanadi cewar, dole ne mace tayi shigar da zata rufe dukkan jikinta.

LEAVE A REPLY