Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama tare da 'ya 'yansa, yayin da yake karbar kyautar talo talo a ranar Sallar godiyar Allah

A ranar kowacce Alhamis din karshe ta watan Nuwamba, muhimmiyar rana ce a kasar Amurka, domin hukumomi kan bayar da hutu ko ina. Amurkawa kanyi tattaki daga gurare masu nisa, domin su koma garuruwansu na asali domin saduwa da dangi da abokai domin yin Sallar godiya ga Allah.

Asali dai wannan biki Amurkawa na yinsa tun kusan shekarar 1621. A wancan lokacin ana yin wannan bikin Sallah ne domin taya juna murnar kammala girbin amfanin gona lafiya, da kuma nuna godiya ga Allah da ya sa amfanin gona yayi kyau, kuma damina tayi harshe.

AMurkawa ssun dauki wannan rana da muhimmanci sama da dukkan wata ranar bukukuwa. Domin hatta kirsimati bata kai wannan rana muhimmanci ba a wajen Amurkawa. Domin miliyoyin talo-talo da aladu ake yankawa aci tare da ‘yan uwa da dangi da iyalai.

Mutum ko ina yake a Amurka, yakan yi kokari ya koma garinsu domin haduwa da ‘yan uwansa dan cin abinci tare don wannan rana. A tarihin kasar Amurka, babu wani biki da kan sanya Amurkawa barin guraren aikinsu su koma garuruwansu donsa sai wannan.

Domin hatta kirsimati a kasar AMurka, hukuma bata bayar da hutun aiki, yayinda a irin wannan rana kuwa ake bayar da hutun kwana biyu ga AMurkawa su koma cikin iyalansu don yin murnar wannan rana.

A yayin bikin wannan rana, ta Sallar godiyar Allah, Amurkawa sun fi mayar da hankali wajen cin abinci tare da iayalai, da cin nama da kabewada kayan makulashe. Haka kuma, Amurkawa kan raba kyaututtuka ga makwabta a irin wannan rana.

 

LEAVE A REPLY