Hoton fasalin maganadisun alcohol oxidase daga halittar fungus ta Pichia pastoris da aka haska da naura mai amfani da fasahar Cryo Electron Microscopy. Masama: Vonck J, Parcej D, Mills D

Daga Abdulrazak Ibrahim

Kungiyar Kimiyya ta Masarautar Sweden (Royal Swedish Academy of Sciences) ta baiwa shehunnan malaman kimiyya Jacques Dubochet da Joachim Frank da Richard Henderson lambar yabo ta Nobel ta kimiyyar Sunadarai, wato Chemistry.

Wannan ya biyo bayan gudummawarsu akan yadda ake iya nazartar ƙwayoyin zarra na molecules ta hanyar anfani da madubin cryo-electron microscopy.

Wannan ɓangaren kimiyya ya baiwa masana damar duba kwayoyin halittu komai ƙanƙantarsu.

Masu bincike na iya amfani da fasahar  cryo-electron microscopy don ganin yadda hada hada ke faruwa a cikin kwayar hallittar cell.

Wannan zai bada da damar fahimtar rayuwa ta fuskar Chemistry da kuma gwaje-gwaje don gano sababbin magunguna.

LEAVE A REPLY