Gwamnan jihar Kaduna malam Nasiru el-Rufai

 

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru el-Rufai ya bayyana cewar zasu kori kusan malaman firamare 20,000  a jihar Kaduna, a cewarsa galibinsu dakikai ne, “mun san cewar za’a kalubalancemu akan korar da zamu yi, amma zamu kashe kunne, mu bar masu korafi suyi korafinsu, amma babu fashi a korar da zamu yi” in ji Gwamna el-Rufai.

Gwamnatin jihar Kaduna ta shiryawa Malaman firamare jarabawa domin fahimtar kwarewarsu, inda aka basu takardun jarabawar ‘yan aji hudu domin su bada amsa, amma kasha biyu bisa uku basu iya amsawa daidai ba.

Gwamna el-Rufai ya kara da cewar, “Mun gwada Malaman firamare kimanin 33,000, inda muka basu takardar yara ‘yan aji hudu su amsa, muka ce kowane malami dole yaci a kalla 75, amma abin takaici, kaso 66 basu iya cin maki 75 ba”.

A dan haka ne, Gwamna yace gwamnatinsa zata salami malaman firamare 20,000, domin a cewarsa sam basu cancanci koyarwa ba, kuma yayi hakan ne domin dawo da kima da martabar ilimi a matakin firamare.

Gwamnan ya kara da cewar gwamnatinsa zata sake dibar sabbin malamai guda 25,000 nan gaba kadan. Yace zasu bi kwakkwafin sabbin malaman da za’a dauka, zasu tabbata baa’a dauki baragurbi ko dakiki ba, a cewarsa wadan da za’a dauka sabbi, sai an tabbatar da kwarewarsukafin daukarsu.

Yace daukar sabbin Malaman a wannan lokacin ya zama dole sabida karancin ingantattun malaman da zasu iya koyarwa a makarantun firamare dake fadin jihar Kaduna.

Shin me zaku ce akan wannan yunkuri na Gwamnan Kaduna?

LEAVE A REPLY