Sarki Salman Bin Abdulaziz Al-Saoud na kasar Saudiyya

Kasar Saudiyya a jiya litinin ta baiwa Najeriya kayan tallafin da suka kai Naira biliyan 3.6 domin rabawa a sansanonin ‘yan gudun hijira dake yankin Arewa maso gabashin Najeriya, wanda rikicin Boko Haram ya daidaita.

Ministan tsaron najeriya, Mansur Dan-Ali shi ne ya bayyana hakan, lokacin da ya karbi tawagar da ta iso najeriya daga kasar Saudiyya domin kawo kayan tallafin, a ofishinsa dake babban birnin tarayya Abuja.

Ya bayyana cewar zasu kafa kwamiti na musamman wanda zasu kula da yadda za’a rarraba kayan tallafin a sansanonin ‘yan gudun hijirarar dake yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Kayan tallafin dai sun kunshi abinci da magunguna da kayan karatu da sauran abubuwan bukatu na yau da kullum domin ragewa ‘yan gudun hijirar radadin halin da suke ciki.

Hukumar kula da bayar da tallafi ta kasar Saudiyya tare da kungiyar Sarki Salman ta bayar da agajin gaggawa ga wadan da suke cikin mawuyacin hali, su ne suka hada wadannan kayayyaki da aka kawo Najeriya domin rabawa ‘yan gudun hijirar.

Tawagar ta iso najeriya ne karkashin jagorancin Nasir Bin Mutlik, mataimakin darakta a hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar saudiyya da Khalid Bin Abdulrahman Al Mani da kuma Muhammad Bin Addidah Al-Namla.

Mista Mutlika ya bayyana cewar Gwamnatin Saudiyya ta bayar da kayan tallafin ne domin agaji da kuma jin kai ga wadan da abin ya shafa, da kuma ragewa Gwamnatin tarayyar najeriya radadin wannan hali da take ciki.

LEAVE A REPLY