Daga Hassan Y.A. Malik

Mayakan kungiyar Al-shabab sun jefe wata mata mai shekaru 30 a duniya a bisa zargin ta da auren maza har sau 11, a cewar mazauna wani gari a kudancin kasar Somalia.

Wannan lamari dai ya faru ne a jiya Laraba.

Mazauna garin mai suna Sablale sun halarci wajen da aka jefe matar mai suna Shukri Abdullahi.

“An gurfanar da Shukri Abdullahi da anihin mijinta da sauran mazaje 9 a gaban kotun kungiyar al-Shabab, inda kowanne daga cikin mazajen ke ikirarin cewa shi ne ainihin mijinta,” Mohamed Usama, gwamnan al-Shabab na yankin Shabelle Lower, ya fada wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Kungiyar al-Shabab dai na daya daga cikin kungiyoyin ta’addanci duniya, inda ta ke ikirarin yunkurin kafa daular Musulunci a kasar Somalia.

Mambobinta sun sha yanke hukuncin yanke hannu ga mutanen da aka kama da laifin sata tare da jefe wanda aka kama da laifin zina.

Hukuncin na su ya na hawa kan maza da mata ne.

LEAVE A REPLY