Morgan Tsvangirai

Morgan Tsvangirai, Jagoran ‘yan adawa a kasar Zambabwe wanda ya sha gwagwarmaya da tsohon Shugaban kasar Robat Mugabe a shekaru da dama, ya mutu a ranar Larabarnan bayan ya sha fama da cutar sankara.

Tsvangirai shi ne ya kafa jam’iyyar MDC a shekarar 1999, jam’iyyar ta zama a sahun gaba wajen nuna adawa ga Shugaba Mugabe akan mulkinsa na lokaci mai tsawo a matsayin Shugaban kasar tun bayan samun mulkin kai da tayi daga hannun turawa.

 

LEAVE A REPLY