Bello Galadanchi

Jaridar Daily Naigerian Hausa ta yi wata tattaunawa ta musamman da hazikin matashi mai himma da kokarin bunkasa harkar kasuwanci da saye da sayarwa ta hanyar amfani da yanar gizo. Wannan matashi Bello Galadanchi, wanda yake zaune a kasar Chana ya kafa wannan kasuwa irin ta ta farko a yanar gizo musammana domin al’ummar Hausawa da kuma masu magana da harshen Hausa. Ga yadda tattaunawarsu da wakilin DNH da shi ta kaya:

DNH: Ko zaka yi mana bayanin wannan kasuwa a takaice?

Bello Galadanchi: To, Bismillahirrahmanir Rahim, Masha Allah, da farko mun yi nazari mungan cewar an dade ana cutar Mallam Bahaushe a wasu bangarori na tattalin arzikinsa da kasuwancinsa, ta yadda ake kwashe masa kafa, tamkar kura da shan bugu; gardi da kwashe dukiya,  wasu baki na mamaye su. To abunda babba ya hango, yaro ko ya hau rimi ba zai hango ba. A matsayi na na yaro, sai na nemi karin sani akan dalilan da yasa Hausawa suke komawa baya a fannoni da dama, a nan ne bincike na ya bayyana abubuwa da yawa kamar rashin iya tafiyar da kasuwanci, da rashin iya tafiyar da shugabanci komai kankantarsa. Ba shakka, wannan babban kalubale ga kowace irin al’umma, domin shi ne abincin da zai ciyar da ita ga, shiyasa muka fara shawarwari akan yadda zamu taimakawa manoman Hausawa sayar da amfanin gonarsu a kasashen waje.

A wannan yunkuri ne, muka gane cewa, akwai rashin mattatara ko ma’adana ta bayanan manoma, da abinda ya shafi kasuwaci da sana’o’in Hausawa. Daga nan ne muka tsara tambayoyin bincike (Questionnaire) muka aikawa jama’a, domin fahimtar bukatunsu, da kuma yadda suke tafiyar da wasu muhimman abubuwan da suka shafi rayuwarsu na yau da gobe. Anan ne muka fahimci abubuwan dake daukar lokacin su, da kuma irin bukatun su. To, zamu iya kawo tsarin da zai hada wadannan batutuwa a waje daya domin samun nasararsu.

Haka kuma, binciken kuma ya nuna mana cewa jama’a musamman matasa da matan aure tsakanin shekaru 18 zuwa 35 suna sha’awar sana’a ko kasuwanci, amma basu da dandali nasu na kansu da zasu koya, ko su koyar da baiwar da Allah ya basu ga al’umma domin bada tasu gudunmuwa. Shafuka kamar Facebook na bayar da dandali na yin talla da koyo, amma abun babu tsari, saboda manhajar zumunta ce. Haka zalika WhatsApp, amma shima bashi da tsari, kuma yana da wahalar samun bayanai da ake nema. To amma kuma jama’a suna sha’awar duka biyun, shi ne muka ce to me zai hana a samar da tsari da jama’a zasu iya tallata hajar su, su kuma ringa sada zumunci suna gaisawa da kokarin sanin juna. Mun yi imanin cewar idan muka gina al’umma mai karfi da jin dadin alherin dake cikin wannan Kasuwa, wannan zai harzuka manufar mu na mayar da Kasar Hausa cibiyar kasuwancin yanar gizo a yammacin Afirka.

A takaice, manufar mu shi ne, amfani da fasaha wajen saukaka rayuwar Hausawa ta hanyar saukaka saye da sayarwa da sufur da samun ilimi da bunkasa fasaha da kiwon lafiya da nufin mayar da ‘yan kasuwa Hausawa mafiya arziki a nahiyar Afirka ta hanyar mamaye wannan fanni kafin ragowa su farga. Masha Allah, alamu na nuna cewa muna kan alkibla mai kyawu. Wannan shi ne a takaice manufar kafa wannan kasuwa tamu a yanar gizo.

DNH: Ka yi mana Karin bayani akan taken da kuke cewa Kasuwar Ku Ce? Ba kune kuka mallake ta ba?

Bello Galadanchi: Da aka ce Kasuwar Bello Kasuwar Ku Ce, wannan ba take bane kawai. Tun kirkirar wannan Kasuwa kasancewar an ga mutane da yawa suna da ra’ayi daya, da kuma sha’awar tsari irin wannan. Tun wannan lokaci, duk wani mataki da aka dauka, sai an tambayi ‘yan Kasuwa sun bada shawarwari, har aka kai ga nan.

Duk wanda yake sha’awar mu’amala da Kasuwar Bello, kofa a bude take, shiyasa muke da ‘yan jarida da marubuta da malamai daban daban saboda suna zuwa domin bada tasu gudunmuwa ga al’umma da kuma nuna irin baiwar da Allah Ya basu. Bugu da kari shago kyauta ne, saboda haka ai babu shakka Kasuwar Bello kasuwar jama’a ce.

DNH: Ko akwai kalubale a wannan aikin?

Bello Galadanchi: Babu shakka muna fuskantar Kalubale. A lokutan baya mun fuskanci lokuta da adadin mutanen dake bukatar mu’amala da Kasuwar Bello da samun kulawa ta musamman ya zarta kiyasin da muka yi a lokacin rubuta tsarin Kasuwar a takarda, dama kuwa babu wanda ya san gaibu sai Allah. Yadda jama’a suka yi rububin shigowa da samun alheri a dan karamin lokaci, wannan ya harzuka mu. Sai dai duk yawan mu da karfin mu, da sababbin hannaye da muke horaswa kafin zuwansu, lokutan basa isa kwata-kwata. Wani lokacin idan ba’ayi sa’a ba, sai suyi zuciya suyi fushi da tafiyar su.

Haka zalika fasahar mu na jawo kalubale, saboda adadin jama’a dake hawa, amma akwai sababbin tsare-tsare masu matukar ban sha’awa da sai an gama gina su baki daya kafin a dora akan yanar gizo. In sha Allah a wannan lokaci, wata sabuwar duniya zata bude a rayuwar yau da gobe ta Hausawa. Muna addu’ar isowar wannan lokaci a halin yanzu da muke aiki babu dare babu rana domin kammalawa akan lokaci. Muna rarrashin ‘yan Kasuwar da suka yi fushi, akan su dawo, zamu kara kaimi da aiki tukuru domin biya muku duka bukatunku.

DNH: Su waye masu taka rawar gani wajen tafiyar da harkokin yau da gobe na Kasuwar Bello?

Bello Galadanchi: Ina, ai wannan tambaya tana bukatar amsa ta musamman. Nima ko da wasa ba zan fara ba, ganin irin girma da bangarori daban-daban na Kasuwar Bello a halin yanzu. A kowane bangare a Kasuwar, akwai wanda yake taka rawa ta musamman kuma shiyasa kullum kasuwar ke kara farin jini da karbuwa a kasar Hausa da sauran kasashen duniya inda akwai Hausawa. Shiyasa zan baiwa duk wanda yake sha’awa shawara akan yayi kokarin shiga groups na WhatsApp na Kasuwar Bello domin kulla alaqa da su.

DNH: Me kuke hasashe Kasuwar Bello zata kasance a shekaru nan gaba?

Bello Galadanchi: Muna kiyasin sama da shaguna dubu dari bakwai da saba’in bisa alkaluma, lamarin da zai janyo hankulan turawa da jama’ar kasashen ketare domin dubawa su nemi irin kayan da babu a wajen su. Anan kaga mun ci nasarar kusantar da mai haja wato kaya da kuma masu saye cikin sauki.

DNH: Wanne fanni kuka fi mayar da hankali akai?

Bello Galadanchi: Eh to, fannin da muka fi mayar da hankali akansa shi ne, na NOMA. Burin kasuwar Bello shi ne samarwa manomanmu na kasar Hausa kasuwar kayan da suka noma inda zasu sayar su ci riba mai yawa, muna son kawar  da batun nan na cid a gumin manomanmu da ake, su sha wahala su noma amfanin gona amma a saya bad a daraja ba a wajensu, amma idan an fitar da kayan aci kazamar riba, su kuma wanda suka yi noma sun kare ba tare da samun wata riba ta ku zo mu gani ba. To muna son yadda manomin da yayi nomansa ya sayar da kayansa da kansa a kasuwar Bello ta hanyar hada shi da masu saye daga kasashen duniya.

Harkar noma na daya daga cikin tushen kafa Kasuwar Bello, kuma dolen-dole mu rike noma hannu bi-biyu saboda a nan karfin mu yake a Kasar Hausa. Kasuwar Bello ta kwan biyu tana shirye-shirye akan tanadin da zai samar da tsarin auna inganci amfanin gona akan wani sikelin da kasashen waje zasu gani su amince da shi. Wannan zai bude hanyoyi masu yawa na sayar da amfanin gona na Hausawa zuwa kasashen waje. To a halin yanzu manoma a Kasuwar Bello basu da yawa sosai, kuma ana bukata su bude shago su tallata kayan su. Wannan zai bamu damar tsara shiri da zai budewa manoma da masu bukata ido ta yadda zasu san inda kaya keda daraja, da kuma inda ake bukata cikin sauki.

 

LEAVE A REPLY