Kudaden ajiya na Gwamnatin Najeriya dake kasashen waje ya karu a watan Janairun nan. Domin kuwa a karon farko asusun ya tara dalar Amurka biliyan 40.4, wadan hakan ke nuna an samu karin dala biliyan 1a watan Disambar da ya gabata kamar yadda Babban bankin kasa CBN ya tabbatar.

Cinikayyar basussukan Najeriya da kuma na takardun lamuni da da Gwamnati ta sayar a shekarar da ta gabata ya taimaka wajen habaka asusun ko takwana na Najeriyar.

Haka kuma, Babban Bankin Najeriya CBN yace, ya kara rubanya kokarinya, inda ya samar da kudi dala miliyan 210 domin habaka cinikayyar Bankunan Najeriya ta kudaden musaya. Babban bankin na yin kokari ne na wadata kananan bankuna da dala domin magance karancinta da ake samu, wanda hakan shi ke haifar da tsadarta.

 

LEAVE A REPLY