Babbar Ministar kudin Najeriya, Madam Kemi Adeosun

Babbar ministar kudi ta Najeriya, Kemi Adeosun ta ce, a cikin mutane miliyan 70 da suka cancanci biyan harajia Najeriya, mutane milyan 40 ne kacal suke iya bina harajin

Madam Adeosun tana bayyana hakan ne a lokacin da ta halarci taron shekara shekara na manyan masana a harkar biyan haraji ta jihar Legas, taron da ake gudanarwa a babban dakin taro na Ade-Ajayi dake jami’ar jihar Legas.

Ta cigaba da cewar, kimanin kashi 13 na ainihin wadan da suke biyan haraji, suke samun rangwamedaga tushe, wanda aka yi tsarin biya haraji kan lokaci ka samu rangwame.

Ministar tace, dole ne sai an sake yin nazari tare da bibiyar tsarin biyan haraji na kasa, domin tabbatar da cewar wadancan mutane miniyan 30 da suke kin bayar da haraji suna biyan nasu harajin kan ka’ida.

Ta kara da cewar: “Ina yawan nanata cewar, me ya sa mutane miliyan 30 suke kin bayar da haraji a Najeriya, wani babban kalubale kan hakan shi ne, ‘yan Najeriya da dama, suna da wasu hanyoyin da suke samun kudade na daban, dan haka suke kaucewa biyan haraji, dan haka ne, suke samun makudan kudade a wasu hanyoyin kasuwanci da wasu boyayyun hanyoyin samun kudinsu.”

A dan haka tace, sabon tsarin biyan harajin da za’a bullo da shi, dole ne ya kunshi masu kasuwanci ta hanyar intanet da kuma masu sana’ar shirya fina-finai, domin su dinga biyan harajinsu ga Gwamnati.

A wajen wannan taro dai, Madam Kemi Adeosun, ta jadda muhimmancin biyan haraji wajen tafiyar da cigaban kasa. Toce dukkan kasashen da suka cigaba, sunda kyawawan tsarin biyan haraji, dan haka Najeriya ma dole ta bi sahun su.

NAN

LEAVE A REPLY