Hassan Y.A. Malik

A wannan makon ma dai, babban bankin Nijeriya (CBN), ya sake sanya dalar Amurka miliyan 210 a kasuwar hada-hadar canji domin wadatar da ‘yan kasuwa da ma duk mabukata dalar Amurka don dakile karancinta a kasuwar canji, wanda hakan ka iya kawo cikas ga harkokin kasuwanci na yau da kullum.

A wata sanarwa da daraktan sadarwa na bankin, Isaac Okorafor ya fitar a jiya Litinin a Abuja, ya ce, an saki dala miliyan 100 ga manyan ‘yan canji masu lasisi don sayar da shi ga mabukata.

Inda su kuma kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa da ake kira da SMEs suka samu dala miliyan 55. Su kuma masu bukatar dalar don biyan kudaden makaranta, biyan kudaden magugunguna ko biyan kudaden asibiti a kasashen ketare da kuma wadanda ke da bukatar dalar a matsalayin alawus dinsu na tafiye-tafiye da ma’aikatu kan tura jami’ansu wato Basic Travel Allowance (BTA), suma suka samu dala miliyan 55.

Okorafor ya dada jaddada manufar babban bankin na tabbatar da samun wadatar dala a kasuwar canji ta yadda za a ci gaba da samun saukin mu’amala da kuma tabbatar da karbabben farashi.

Ya ci gaba da cewa, CBN zai ci gaba da gudanar da kasuwar canji ta hanyar rage adadin kayan masarufin da ake shigo da su daga waje tare kuma da kara karfin taskar kasar na kudaden waje.

Ko a ranar 12 ga wannan watan ma dai sai da CBN ta saki dala Amurka miliyan 210 don biyan bukatun dalar da ‘yan kasar ke da su a bangarori daban-daban na mu’amalar yau da kullum da kuma cinikayya.

Har yanzu dai Naira ta tsaya a darajarta na N30 a kowace dalar Amurka a kasuwannin canji na bayan fage.

LEAVE A REPLY