DR.maikanti K. Baru Shugaban kamfanin mai na kasa NNPC

Babban kamfanin mai na  ƙasa NNPC, yace yana yin dukkan mai yuwuwa wajen ganin ya wadata  ƙasarnan da albarkatun man fetur nan ba da jimawa ba, domin magance matsanancin  ƙarancin man da ake fama da shi a sassan  ƙasarnan.

Masu ababen hawa da matafiya, suna shan fama da baƙar wahala sakamakon fama da  ƙarancin man fetur din da ake yi, wanda aka shafe makonni biyu ana fama a kusan ko ina a fadin Najeriya.

Kakakin Kamfanin mai na ƙasa Nda Ughamadi, ya bayyanawa manema labarai a ranar Asabar cewar, tuni kamfanin ya fara tura man zuwa manyan kasuwannin dillancinman fetur guda shi a fadin Najeriya, kasuwannin sun hada da, Total da Forte Oil da MRS da Oando da 11 plc da kuma NIPCO plc.

Wadannan kamfanoni,suna nan suna yin lodin man daga babbartashar mai dake Legas zuwa dukkan sassan Najeriya inda wadancan kamfanoni ke da kasuwanninsu na kasuwancin man fetur din.

“Kar a manta tuni, NNPC ta shigo da tataccen mai a manya manyan jiragen dakon mai wanda yanzu haka suna nan maƙare da mai akan teku, kuma za’a yi saurin rarraba shi ga dukkan sassan Najeriya domin magance matsalar karancin man”

“Haka kuma, wannan tataccen man za’a aika da shi dukkan matatun man da muke da su a Najeriya, ta yadda za’a dinga yin dakonsa daga kowacce matata cikin sauki ba sai an zo babbar tashar man ba”

“A dan haka NNPC ke gargadin masu boye man domin tunanin samun kazamar riba, da su sani cewar, jami’an tsaro suna nan suna suntiri, duk gidan man da aka samu da laifin bauye shi da nufin samun kazamar riba, to su sani zasu kuka da kansu”

Tuni dai Shugaban kamfanin NNPC na ƙasa Maikanti Baru ya tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewar, yanzu haka akwai mai kimanin lita biliyan daya da aka shigo da shi ƙasarnan, wanda yanzu haka yana kan teku ana ƙoƙarin sauke shi.

Baru ya kuma tabbatar da cewar, za’a ninka adadin man da ake aikawa dukkan sassan kasarnan domin rarraba shi ga tashoshin samarda man dake ko ina a fadin Najeriya, a sabida haka ne, yayi kira ga ‘yan Najeriya da su kara hakuri, domin matsalar ta zo karshe.

LEAVE A REPLY